Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Ƙetare

Shugabannin duniya sun fara taron zaman lafiya a Paris

Published

on

An buɗe taron samar da zaman lafiya da ya haɗa shugabanin ƙasashen duniya a birnin Paris na Faransa.

Taron dai ana kyautata zaton zai taimaka wajen samar da hanyoyin warware wasu daga cikin tarin matsallolin da suka addabi duniya.

Shugabannin za su shafe tsawon kwanaki uku suna tattaunawa dangane da batutuwa da dama da suka haɗa da muhalli da lafiya da na’urar zamani.

Ɗaya daga cikin batutuwan da zai fi ɗaukar hankulan shugabanin shi ne na tantance hanyoyin kawo ƙarshen annobar cutar Covid19.

Daga cikin shugabanin ƙasashen da ake sa ran za su bada gagarumar gudunmawar magance matsalolin har da shugaban Senegal Macky Sall da shugaba Mohammadu Buhari da mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Haris sai mai masaukin baƙi Emmanuel Macron.

Ana kyautata zaton mutane  dubu 15 za su kasance kai tsaye ta intanet domin kallon yadda taron zai kasance, yayin da mutane 350 za su kasance a zauren taron kuma daga cikinsu har da shugabanin ƙasashen Duniya 30, 12 daga Afrika.

 

RFI

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!