Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Abin da tsohon shugaban ƙasar Najeriya Buhari yayiwa kano abin a yaba ne -ACF

Published

on

Ƙungiyar tuntubar juna ta Arewa Consultative Forum ta ce abin da tsohon shugaban kasar Najeriya General Muhammad Buhari yayiwa jihar Kano abin a yaba ne wajen samarwa da jihar abubuwan ci gaba da zasu ingata rayuwar al’ummar jihar dama ƙasa baki ɗaya.

Shugaban ƙungiyar reshen kano Dakta Gwani Farouk Umar ne ya bayyana hakan yayin wata ziyara da ƙungiyar ta kaiwa tsohon shugaban ƙasar Najeriya General Muhammad Buhari gidan sa da yake a Daura.

Dakta Gwani Farouk ya kuma ce la’akari da irin abubuwan da suka haɗar da layin dogo da ya tashi daga kano zuwa Kaduna kano zuwa Daura da kuma bututun gas da aka janyo zuwa kano da sauran wasu ayyuka to ya zama wajibi wannan ƙungiyar reshen kano ta yaba masa.

Da yake jawabi tsohon shugaban ƙasar Muhammad Buhari godewa ƙungiyar yayi bisa ziyara da suka kawo masa, inda yayi fatan ƙungiyar zata mayar da hankali wajen kawowa arewa ci gaba da ƙasa baki ɗaya.

Yayin ziyarar ƙungiyar ta sami rakiyar mambobin ƙungiyar dake jihar kano dama ƙasa baki ɗaya domin ƙara godewa tsohon shugaban ƙasar na Najeriya Muhammad Buhari.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!