Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Abinda Kwankwaso ya fadawa Buhari a wasikarsa

Published

on

Tsohon gwamnan jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya aikewa da shugaban kasa Muhammadu Buhari wasika dangane da halin da ake ciki a jihar Kano.

Wasikar tsohon gwamnan ta fara ne da mika ta’aziyyar sa ga shugaban kasa Muhammad Buhari bisa rashin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa marigayi Malam Abba Kyari, wanda ya rasa ransa sakamakon annobar cutar Corona daya kamu da ita.

Kwankwaso yace ya rubuta wasikar ne bisa wasu dalibai guda biyar.

Ya ce tun daga lokacin da aka samu bullar cutar Corona a jihar Kano aketa samun yawan mace-macen al’umma a fadin jihar a kowacce rana.

Tun daga lokacin da gwamnati ta fara daukan matakan dakile cutar a jihar Kano ta sanya dokar hana zirga-zirga a fadin jihar tare da rufe hanyoyin shigowa da fita garin na Kano.

Rabi’u Musa Kwankwaso, ya kuma ce gwamnati batayi amfani da kwararru ba wajen bincikar musabbabin yawan mace-macen da ake samu a jihar Kano.

Ya kuma ce babu alaka mai karfi tsakanin gwamnatin jihar Kano da gwamnatin tarayya wajen lalubo hanyoyin da za’a magance yakar cutar Corona a jihar ta Kano.

Ta cikin wasikar Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce akwai firgici da tsoro a harkokin lafiyar jihar Kano ta yadda aka kasa samarwa da ma’aikatan lafiya kayan aikin daya kamata wanda hakan ne ya sanya ma’aikatan ke nuna tsoro wajen gudanar da ayyukansu.

Kazalika Kwankwaso ya ce dole ne al’ummar jihar Kano su bayar da gudummuwar da ta dace wajen yaki da cutar ta Corona, don ganin an maganceta a kasa baki daya.

Rabi’u Musa Kwankwaso yace yana so yaja hankalin shugaban kasa Muhammad Buhari da cewa ya mayar da hankalin sa zuwa jihar Kano wajen gudanar da cikakken binciken hakikanin abinda ke haddasa yawan mace-mace a jihar Kano musamman ga mutane masu yawan shekaru.

“Makonni biyu kenan da fara samun mace-macen amma har yanzu gwamnati bata dauki matakin daya kamata ba wajen gudanar da binciken musabbabin abin da ke kawo mace-macen.” A cewarsa.

Har ila yau, Kwankwaso ya ce cikin makonni biyu an binne daruruwan mutanen da suka rasu a kananan hukumomi takawas dake cikin birnin Kano wanda ba’a taba samun  irin hakaba a wannan lokacin wanda yasa al’umma ke zargin mutuwar mutanen nada alaka da cutar Corona.

Rabi’u Kwankwaso ya kuma bayyana takaicin sa bisa yadda gwamnatin jihar Kano ta fito ta karyata yawan mace-macen da ake samu a Kano ba tare da ta gudanar da kwakw-kwaran binciken daya kamata ba.

Kwankwaso ya ce jihar Kano na daya daga cikin jihohin dake da yawan al’umma a kasar nan kuma birnin Kano na daya daga cikin birni mafi girmna a Afrika adon haka yakamata masana da kwararru su maida hankalin su a jihar Kano wajen bincikar musabbabin abinda ke faruwa na mace-macen mutane.

Tare da samar da kayan aikin da suka kamata domin a yaki cutar Corona dake kara Kamari a jihar ta Kano duba da yawan al’ummar dake zaune a garin.

A karshen takardar tasa Kwankwaso yace wadannan dalilai ne suka sanya ya rubutawa shugaban kasar takarda domin sanar dashi gaskiyar abinda ke faruwa a jihar Kano.

Ya kuma ce yana fata shugaban kasa Muhammad Buhari zai la’akari da abubuwan daya zayyana ta cikin wasikar tasa domin kawowa jihar Kano dauki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!