Labarai
SERVICOM ta sha alwashin bibiyar korafi kan katin sheda ga masu kula da marasa lafiya a AKTH

Hukumar tabbatar da inganci da nagartar ayyukan ma’aikatan Gwamnati SERVICOM, ta sha alwashin bibiyar duk wani korafin da ya shigo gabanta kan sabon tsarin bayar da katin sheda ga masu jinyar yan uwansu a Asibitin koyarwa na Aminu Kano da aka fito da shi don inganta tsaro da kula da marasa lafiya.
Mukadashin Darakta a hukumar tabbatar da inganci da nagartar ayyukan ma’aikatun gwamnati SERVICOM reshen Asibitin koyarwa na Aminu Kano Abdul Muhammad, ne ya bayana hakan a zantawarsa da Freedom Rediyo.
Inda ya tabbatar da cewa, tsarin bayar da shida ga masu jinyar yan uwansu a Asibitin Aminu Kano ya tafi yadda aka tsara shi ba tare da musguna wa kowanne bangare ba tsakanin masu jinya da ma’aikatan Asibitin.
You must be logged in to post a comment Login