Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

An samu karin mutum 46 dauke da cutar Corona a Kano

Published

on

Gwammatin jihar Kano ta tabbatar da cewa a ranar Lahadi an samu karin mutane 46 dake dauke da cutar Coronavirus a jihar.

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta sanar a shafinta na Twitter da misalin karfe 11:45 na daren Lahadi cewa sakamakon gwajin da aka yiwa mutane 486 ya nuna cewa 46 daga ciki suna dauke da cutar ta Corona.

Sannan an sallami karin mutane 27 da suka warke daga cutar.

Yazuwa yanzu mutane 1,137 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a jihar Kano baki daya, cikin mutane 8,181 da aka yiwa gwajin cutar a jihar.

Sanarwar ma’aikatar lafiya ta Kanon ta kuma tabbatar da cewa zuwa yanzu mutane 626 ne suka warke daga cutar Corona a jihar.

Sai mutane 50 da suka samu shahada sanadiyyar cutar a Kano.

Yanzu haka masu dauke da cutar Corona 461 ne ke cigaba da samun kulawar jami’an a lafiya a cibiyoyin killace masu dauke da cutar dake Kano.

Wannan na zuwa ne yayin da gwamnatin Kano tayi nisa wajen yin gwajin cutar Corona gida-gida a jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!