Labarai
Abinda ya sa Zulum ya ce NEMA ta hanzarta bada tallafi ga ‘yan gudun hijira
Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum ya bukaci hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA da ta hanzarta tallafawa mutanen da rikici ya raba da gidajensu da ke cikin mawuyacin hali a yanzu.
Mashawarci na musamman ga gwamnan kan harkokin yada labarai Malam Isa Gusau ne ya sanar da hakan yau a Maiduguri, inda ya ce mutane sama da dubu dari takwas ne rikicin ya raba da gidajensu, wadanda yanzu haka suke bukatar tallafi matukar.
Sanarwar ta ce gwamna Zulum ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci ofishin shugaban hukumar ta NEMA Abuja Air Vice Marshal Muhammadu Alhaji Muhammad mai ritaya.
Sansanonin ‘yan gudun hijirar suna garuruwan Monguno da Bama da Damboa da Gwoza da Dikwa, sai Gamboru Ngala da Damasak da Banki da Pulka da kuma Gajiram.
You must be logged in to post a comment Login