Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Abinda ya sanya ‘yan adai-daita sahu janye shiga yajin aiki

Published

on

A yau jumu’a ne direbobin baburan adai-daita sahu na jihar Kano suka kudiri aniyar tafiya yajin aiki da kuma zanga-zanga, sakamakon harajin kudi har naira dubu ashirin da shida da hukumar KAROTA ta sanya musu.

Sai dai biyo bayan wani zaman sulhu da shugabannin kungiyoyin ‘yan adai-daitar sukayi da shugaban hukumar KAROTA an cimma matsaya, inda akayi yarjejeniyar cewa direbobin zasu biya naira dubu takwas-takwas kafin karshen watan disambar da muke ciki.

Tunda farko dai hukumar KAROTA ta kudiri aniyar rage yawan direbobin adai-daita sahun ne, ka sancewar sunyi yawa a gari fiye da kima, domin kuwa duk inda ka zaga, zaka hangi kalar ruwan dorawa irin ta baburan wadda kuma tayi kama da kayan sarki irin na jami’an Hukumar ta KAROTA.

Baya ga hakama dai hukumar KAROTA na zargin wasu daga direbobin na KAROTA na aikata wasu munanan laifuka.

Sai dai a karshe shuwagabannin ‘yan adai-daita sahun sun amince da janye yajin aikin da kuma zanga-zangar da suka shirya farawa a yau jumu’a, sai dai an jiyo wani tsagin kungiyoyin ‘yan adai-daita sahun na Kano na cewa suna nan akan bakansu, don haka basu gamsu da waccan maslaha ba kuma zasu tsunduma yajin aikin a yau.

Allah ya kyauta.

Labarai masu alaka:

Gwamanatin Kano za ta rage yawan baburan adaidaita sahu

Hukumar KAROTA ta nemi a kebe mata Naira biliyan guda

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!