Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tashar freedom rediyo na wayar da kan mutane –Sarkin Alkalman Kano

Published

on

Sarkin Alkalman Kano Alhaji Iliyasu Labaran Daneji ya bayyana gidan Redio Freedom a matsayin daya tilo a Arewacin Najeriya dake koyar da kowane fanni daya shafi rayuwar dan Adam musamman wajen wayar da kan mutane su san hakkinsu.

Alhaji Iliyasu Labaran Daneji ya bayyana hakan ne a wani bangare na taya gidan radio Freedom murnar bikin cikarta shekaru goma sha shida da kafuwa.

Sarkin Alkalma ya kuma kara da cewa Redio Freedom tazama tamkar mudubin sauran kafafen yada labarai  a Arewacin kasar nan wajen koyon shirye shirye masu amfani ga jama’a domin warware musu matsalolin su kai tsaye harma da Ilmantarwa fadakarwa da nishadantarwa.

Guarantee Radio ta sha da kyar a hannun Freedom Radio

Freedom Radio za ta buga wasan sada zumunci da Road Safety

Guarantee Radio ta sha da kyar a hannun Freedom Radio

Alhaji Ilyasu Labaran Daneji ya nanata cewa babban abunda ya daukaka gidan Radio Freedom bai wuce yadda ma’aikatanta suka mayarda hankali wajen nemawa marasa lafiya tallafi domin neman lafiyarsu , don haka suna rokon Allah ya cigaba da tallafawa gidan ya kuma cigaba da daukakashi a idon duniya.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito cewa Sarkin Alkalman Kano Iliyasu Labaran Daneji na fatan Radio Freedom zasu cigaba da rike kambun su musamman wajen gudanarda shirye shiryen da suka shafi jama’a kai tsaye.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!