Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Abin da yasa muke hada auratayya a tsakanin mu-Kungiyar Tagwaye

Published

on

Kungiyar tagwaye ta jihar Kano ta ce za ta ci gaba da samar da hadin kai da taimakon juna tsakanin tagwayen dake fadin jihar Kano.

Shugaban kungiyar Injiniya Hassan Ahmad Ma’kari ne ya bayyana hakan yayin taron walimar auren sa da Hassana Muhammad Lawan da aka gudanar yau Laraba 29 ga watan Satumbar shekarar 2021.

Ya ce makasudin kafa kungiyar shine ganin an samar da zuminci da hada auratayya tsakanin Tagwayen dake ciki da wajen jihar Kano”.

 

Injiniya Hassan Ahmad Ma’kari ya kara da cewa “tsawon shekaru hudu da kafa kungiyar mun samu nasarar aurar da Tagwaye a tsakanin mu karo 4 kuma mun kara samar da hadin kai a tsakanin mu”.

Hassan Ahmad Ma’kari ya kuma bukaci dukkanin tagwayen dake fadin jihar Kano da su shigo kungiyar domin kara samar da zuminci a tsakanin su.

Taron dai ya samu halartar Tagwaye dake ciki da wajen jihar Kano inda sukazo suka nuna farin cikin su game da auren.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!