Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kungiyar tagwaye na yaki da barace-barace tare da ‘yan biyu a Kano

Published

on

Kungiyar ‘yan tagwaye ta kasa dake nan jahar Kano  wacce ake kira da Tagwe forum ta sha alwashin kawo karshen barace-barace da wasu iyayen ‘yan biyun ke yi da su a  titinan kasar nan saboda rashin karfi yadda zasu kula da su.

Shugaban kungiya injiniya Hassan Ahmad Makari ne ya bayyana hakan ya yin ziyarar kulla alaka da suka kawo nan tashar Freedom Radiyo a yau Talata.

Inginiya Hassan Ahmad  ya ce sun kafa kungiyar ne a kokarinsu na ganin sun samar da ingantattaciyar rayuwa a tsakanin su musamman ta bangarorin karatu da sana’a da kuma auratayya.

Da yake jawabi shugaban tashar Freedom Radiyo Kano Malam Ado Sa’idu Warawa ya ce Freedom Radiyo zata baiwa kungiyar ta Tagwaye gudunmaw a wajan ganin sun ciyar da al’umma gaba.

Wakiliyar mu Aisha Shehu Kabara ta ruwaito cewar kungiyar ta ‘yan Tagwaye tayi kira ga iyayen yaran da basu da karfin kula da yaran da su nemi kungiyar domin tallafa musu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!