Labarai
Abubakar Malami ya musanta zargin da EFCC ke masa na mallakar asusun banki 46

Tsohon ministan shari’a Abubakar Malami, ya musanta zargin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ke yi masa na cewa yana da asusun banki har guda 46 da aka bude su ba bisa ka’ida ba.
Abubakar Malami ya yi wannan martanin ta bakin mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai Bello Doka, inda ya ce Malami bai da wata alaka da kudaden da suka fito daga tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha, kuma bai taba yin wani laifi na kudi ba kamar yadda EFCC ke zargi.
Ya kara da cewa, tsohon ministan yana da asusun banki guda shida ne kacal, kuma EFCC ta san da su.
You must be logged in to post a comment Login