Coronavirus
Abubuwa 8 da Kwankwaso ya nemi gwamnati tayi a wasikarsa
Cikin wata wasika da tsohon gwamnan Kano Injiniyya Rabi’u Musa Kwankwaso ya rubutawa shugaban kasa Malam Muhammadu Buhari ya nemi gwamnati da tayi wadannan abubuwa guda takwas da ya lissafo.
1. Na farko dole sai gwamnatin tarayya ta shiga cikin lamarin domin ceto rayukan mutane sama da miliyan 10 dake zaune a jihar Kano domin akwai bukatar duba halin da a ke ciki.
2. Gwamnatin tarayya ta kasance ita ce da alhakin kula da al’amuran da su ka shafi cutar a jihar Kano.
3. Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamiti mai inganci a kan yaki da cutar Covid-19 wanda dukannin mambobin sa kwararru ne a harkarkar wanda za su duba al’amarin.
4. A kalla sai an samar da cibiyoyin gwajin cutar guda biyar tare da wuraren daukar gwajin cutar guda 10 a jihar Kano.
5. Sannan kwamitin karta kwana ya horas da jami’an lafiya ta yadda zai rinka karbar kididdigar adadin mace-macen da a ka yi a dukannin makabartun jihar Kano, haka zalika sauran jami’an lafiya su bincika wajen ganin sun san musabbabin mutuwar da a ka yi a Kano.
Sannan su duba dukannin marasa lafiya tare da wadanda su ka ziyarci jana’iza wajenn ganin an tattaro su an kuma killace su baki daya domin yi musu gwaji.
6. Duk da an karyata adadin mutanen da su ka mutu, wannan mace-macen da a ka yi ba mamaki su na da alaka ko dai cutar Covid-19 ko kuma wata cutar ta daban, domin haka gwamnatin jiha da ta tarayya dole sai sun duba wannan lamarin mace-macen da ta duba kan musabbabin ta, sannan dukannin masana a harkar lafiya sai sun duba a duk lokacin da a ka samu wani ya mutu.
7. gwamnatin tarayya ta turo kwararrun jami’an lafiya wadanda za su bincika a kan mace-macen da a ka samu a jihar Kano.
8. Tallafin kamata ya yi ya zaman a kowa da kowa kamar yadda matsalolin yunwa da talauci da cutar ta haifar ba wai sun takaita ga iya ‘yan wata jam’iyar siyasa ba.
You must be logged in to post a comment Login