Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Abubuwan da baku sani ba game da soyayyar Sulaiman da Janine

Published

on

Labarin soyayyar matashi Sulauman Isah da kuma dattijuwa Janine Ann Reimann-Sanchez labari ne da ya karade duniya a wannan makon da muke ciki, kan haka ne Freedom Radio ta bibiyi wannan soyayya daga tushenta, wato dandalin sada zumunta na Instagram.

Bayanai a shafin Sulaiman na Instagram na nuna cewa soyayya ta fara karfi a tsakanin masoyan ne a ranar 7 ga watan Mayu na shekarar 2019 inda Sulaiman ya wallafa hotonta a shafinsa na Instagram tare da cewa “Labarin rayuwa ta ba zai taba cika ba, sai tare dake masoyiyata, Ina kaunarki baby na”

Nan take madam Janine ta mayar da martani irin na masoya inda ta ce “Ina kaunarka sosai Baby”.

Sulaiman ya rufe tattaunawar da alamar nan ta soyayaya wato love ? sannan ya lika masa alamar ? cikin ?mutane goma sha biyu ne kacal sukayi liking wannan hoto da Sulaiman ya wallafa.

A ranar 11 ga watan Mayu na shekarar 2019 Sulaiman ya wallafa wani hotonsa a shafin na Instagram, kan kace kwabo tuni Madam Janine ta garzayo inda tayi tsokaci akan hoton da cewa “Kyakykyawan mutumina, Ina kaunarka,”.

Nan take Sulaiman ya mayar da martani da cewa “Ina matukar kaunarki Mata ta, kuma abar kaunata”.

Mutane goma sha daya ne kacal sukayi liking wannan hoto.

Daga nan ne duk wani hoto da Sulaiman ya wallafa Janine ce kan gaba wajen danna masa alamar nuna sha’awa wato like ko kuma muce Love a yaren Instagram.

Kazalika Sulaiman ya cigaba da wallafa hotunan Janine a shafinsa dauke da zafafan kalaman soyayya inda yake kiranta da “Matata”.

Sulaiman na da mabiya 125 a shafin na Instagram sannan ya wallafa bayanai wato posting sau 21 kacal.

Da muka leka shafin Instagram na amarya Janine kuwa mun iske shi da kalaman nuna tsantsar kauna ga Sulaiman a farfajiyar shafin.

Sai dai asusun nata yana cikin tsarin nan na sirri wato Private Account wanda ba zamu samu damar ganin abubuwan da ta wallafa ba har sai ta amince, don haka muka tura da neman amincewa daga gareta, inda muke jiran tsammani.

Amarya Janine tana da mabiya 67 kacal a Instagram sannan ta wallafa bayanai wato posting guda 35 kacal.

Har ila yau acikin tattaunawar masoyan da muka ci karo da ita mun gano cewa tuni Sulaiman ya fara koyar da ita yaren Hausa domin kuwa ko a watan Yuli na shekarar 2019 ya sanya hotonta inda yayi jawabi cikin harshen turanci yayinda ita kuma ta bashi amsa cikin harshen Hausa.

A ranar Alhamis da ta gabata ne gidan Rediyon Freedom ya fara kawo labarin cewa Janine tayo tattaki daga kasar Amurka domin neman auren wannan matashi.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!