Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda masarautar Kano ta dakatar da mai Unguwa kan saida jariri 

Published

on

Majalisar masarautar Kano ta dakatar da mai unguwar Sabon gari dake karamar hukumar Fagge Alhaji Ya’u Mohammad saboda  zargin yana da hannu wajen saida wani yaro dan shekara daya.

Mai unuwar ta sabon gari wanda ya ake zargin da saida yaron ta hannu kwamandan Hisbah na karamar hukumar Hisbah ta Fagge Jamilu Yusuf.

Wannan na kunshi cikin sanarwar da sakataren galadiman Kano Abbas Sunusi, Muhammad Umar ya fitar a madadin majalisar masarautar Kano cewa an dakatar da dagajin Alhaji Ya’U Mohammad kan zargin wannan badakalar a jiya Talata.

Muhammad Umar ya ce majalisar masarautar  Kano ta yanke shawarar dakatar da mai unguwar ne har sai hukumar hana safara da fataucin bil adama ta kasa NAPTIP  ta kammala bincike.

Hukumar NAPTIP na binciken dagacin karamar hukumar Fagge Alhaji Yau Mohammad tare da kwamandan Hisbah na Faggen Jamilu Yusuf kan zargin saida jariri ga wata mace kan Naira dubu 20.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!