Connect with us

Coronavirus

Abuja ta zarce Kano yawan masu Coronavirus

Published

on

Jihar Kano ta dawo ta uku a yawan masu cutar Coronavirus a Najeriya, yayinda birnin tarayya Abuja ta dawo ta biyu.

Mutum 1092 aka tabbatar sun kamu da Covid-19 a Abuja, inda Kano aka samu adadin mutum 1025.

Har yanzu Legas ce kan gaba a Najeriya, da kididdigar NCDC ya tabbatar da cewa mutum 6266 suka kamu da ita a jihar.

Mutane 13,873 suka kamu da cutar Coronavirus a fadin Najeriya, an sallami 4,351 bayan da aka tabbatar sun warke, yayinda 382 suka rigamu gidan gaskiya.

A farkon bullar cutar dai birnin tarayya Abuja ce ke mataki na biyu kafin daga bisani jihar Kano ta zarce ta, sai kuma a yau ta kara kerewa jihar Kanon.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!