Labarai
Abun da ya sanya NUPENG dakatar da rarraba man fetur a Legas
Kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta kasa NUPENG ta bai wa mambobinta da ke shiyyar Lagos umarnin dakatar da rarraba man fetur a jihar Lagos da kewaye daga jibi litinin.
Kungiyar ta NUPENG, ta ce ta dau wannan mataki ne biyo bayan zargin da ta yi na cewa manyan motoci dauke da kwantainoni sun cunkushe hanyoyin da ke cikin Lagos wanda hakan ke zama barazana ga mambobinta.
Haka zalika kungiyar ta kuma bayyana cewa rashin kyawun tituna da yawan karbar na goro da jami’an tsaro ke yi a wajen mambobinta na daga cikin dalilan da ya sanya za ta dauki wannan mataki.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar ta NUPENG, Prince Willaims Akporeha da sakataren kungiyar Olawale Afolabi, ta ce matukar ana so su dawo bakin aiki to sai hukumomi sun dauki matakai kan wadannan matsaloli da kungiyar ta zayyana.
Masu lura da lamuran yau da kullum dai na ganin cewa, wannan mataki ka iya janyo karancin man fetur a kasar nan baki daya.
You must be logged in to post a comment Login