Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun shirya ci gaba da tsaftace kasuwar Sabongari – Uba Zubairu

Published

on

Hukumomi a kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi da aka fi sani da kasuwar Sabongari a nan Kano, sun ce, za su yi iya kokarinsu wajen ganin cewa, ciki da wajen kasuwar sun kasance a ko da yaushe a yanayi mai tsafta.

Manajan darakta na kasuwar Alhaji Uba Zubairu Yakasai ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai.

Alhaji Uba Zubairu Yakasai ya kuma bukaci ‘yan kasuwar da dukkan nin masu ziyartar kasuwar da su kasance suna sanya takunkumin rufe baki da hanci a duk lokacin da za su shiga kasuwar don kare kai daga cutar corona.

Manajan darakta na kasuwar ta Sabongari, ya kuma bukaci ‘yan kasuwa da su rika biyayya ga dokokin da aka sanya musu wajen rufe shagunansu da misalin karfe shida na yammaci, domin kuwa duk wanda aka kama shagonsa a bude bayan karfe shida za a hukuntashi.

Da ya ke gabatar da jawabi, daraktan mulki na kasuwar, Alhaji Muhammad Bashir Mai-Unguwa, kira yayi ga ‘yan kasuwar da su hada kai don bunkasa harkokin tattalin arziki a kasuwar da ma jihar Kano baki daya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!