Manyan Labarai
Kafafan sada zumunta na barazana ga matasa – Muhammad Yahaya
Wani dattijo a unguwar Danrimi dake rijiyar lemo Alhaji Muhammad Yahaya ya bayyana takaicin sa kan yadda da yawan matasa ke maida hankali kan harkokin wasanni da kuma amfani da kafafen sadarwa na zamani fiye da mayar da hankali wajen yin abubuwan da zasu amfane su wanda hakan ke barazana ga gurbacewar tarbiyyar su.
Alhaji Muhammad Yahaya ya bayyana haka ne a yayin taron saukar karatun Alqur’ani mai girma na madarasatul tahfizul qur’an watazakiyyatul adfal.
Ya kara da cewa ya zama wajibi iyaye su mai da hankali wajen baiwa ‘ya’yan su ilimin addinin musuluci domin ta haka ne kadai al’ummar musulmi zasu fita daga halin da suke ciki na tabarbarewar zamani.
A nasa bangaren shugaban makaranta ta madarasatul tahfizul qur’an Watazakiyyatul adfal Malam Abdullahi Usman yace makaranta ta shafe shekara Ashirin da uku ba tare da cikakken matsuguni ba inda yayi kira da gwamnati da mawadata dasu tallafawa makarantar da matsuguni.
Wata kungiya ta shirya babban taron matasan jihar Kano
Dogaro da kai tsakanin matasa shi ne maganin rashin aikin yi
‘Yan sanda sun kama mai damfarar matasa
Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa dalibai gona sha uku ne suka sauke da suka hada da maza da mata.