Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Abunda ya kamata ku sani kan Tasirin yada labarun karya yake

Published

on

A ‘yan kwanakin nan ne dai wasu fayafayen bidiyo suka karade shafukan sada zumunta na zamani a kasar nan kan cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kara aure, da ministarsa ta ma’aikatar ayyukan jin kai da kare aukuwar ibtila’i wato Hajiya Sadiya Umar Farouk.

Kafin wannan labari ma an yi ta yada jita-jitar cewa uwargidan shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari ta yi yaji, sakamakon kara auren da maigidanta zai yi.

Haka kuma dai, an kuma wallafa wani bidiyo da ke nuna Hajiya Aisha Buhari na yin fada sakamakon rufe mata wani bangare na gidanta.

Bata tsaya a kan ‘yan siyasa kadai ba, domin ko irin wannan ta faru ga sanannen malamin addinin musuluncin nan Malam Aminu Ibrahim Daurawa, bayan da aka wallafa wani bidiyo da ke nuna wani yana tikar rawa da wata mata, amma aka Malam Daurawa ne.

Ire-iren wadannan rahotanni su na da yawa ga mashahuran mutane, sai dai abin takaicin shi ne ta yadda lamarin ke kara ta’azzara, maimakon sauki, har ma masana halayyar ‘dan adam ke bayyana hakan da yawaitar kafafen sadarwa na zamani da kowa yake iya mallaka.

To ko yaya mutane ke kiyaye kansu ga yada irin wannan labari? Da kuma yadda za’a magance matsalar, wasu mutane da Freedom Radio ta zanta da su sun bayyana ra’ayoyinsu kamar haka.

Malam Muhammad Hamisu Sharifai, wanda ya kasance dalibi mai karatun digiri na uku wato digirgir a bangaren na’ura mai kwakwalwa da kuma gano masu aikata laifuka ta internet, ya bayyana cewa rashin daukar mataki a kan masu aikata irin wannan laifi na taka rawa wajen kara ba su damar ci ga da aikatawa.

Ya kara da cewa, matukar ana son magance matsalar to ya zama wajibi hukumomi da gwamnatoci su dauki matakan da suka dace a kai.

Yada labaran karya wani lamari ne da a yanzu ya zama ruwan dare game dunuiya, musamman ma idan aka yi la’akari da kafofin sadarwar zamani ke tashe, wadanda suka kasance hanyoyi masu sauki da masu kirkirar labaran karya ke amfani da su wajen yada su.

Babban abin damuwa game da labaran karya bai wuce yadda a yanzu wasu ke kirkirar labaran kareya a kan mutane masu kima da daraja a idon duniya, da suka hadar da malamai da sarakuna har ma da ‘yan siyasa.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!