Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan sanda sun yiwa mutanen Bichi alkawari

Published

on

Mai martaba sarki bichi Alhaji Aminu Ado Bayero ya ja hankalin Al’ummar kasar nan  da su maida hankali wajen taimakawa  jami’an ‘yan sanda.

Mai martaba sarkin Bichi ya bayyana haka ne lokacin da Kwamishinan ‘yan sanda na jihar kano CP Ahmad Iliyasu tare da hadin gwiwar ‘yan sandan cikin alumma suka kai masa ziyara a fadar sa dake garin Bichi.

Aminu Ado Bayero ya kara da cewar a al’ummar sa a shirye suke da su baiwa ‘yan sanda hadin kai domin a gano bata gari da suka addabi jama’aa karamar Bichi.

A nasa jawabin kwamishinan ‘yan sanda CP Ahmad Iliyasu yace zai taimakawa Masarautar ta Bichi da al’ummar baki daya wajen karfafa tsaro, da kuma bankado bata gari a ciki da wajen jihar Kano baki daya.

Kazalika CP Ahmad Iliyasu ya kara da cewa dole ne jama’a su taimaka musu don gano masu laifi a jihar nan dama kasa baki daya.

Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa Al’umma yankin a shirye suke da su baiwa ‘yan sanda hadin kai don gano bata gari a cikin Al’umma.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!