Labarai
ACF ta karyata bidiyon da ke cewa ta na goyon bayan yi wa yan ta’adda afuwa

Kungiyar tuntuba ta Arewa ACF, ta karyata wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda ke zargin ta da goyon bayan yi wa ’yan ta’adda da ’yan bindiga afuwa.
Ta cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta ce maganganun sun samo asali ne daga wata hira da Wazirin Dutse, Alhaji Bashir Dalhatu, ya yi, amma aka yanke ta kuma an fassara ta ba dai-dai ba domin cimma wata manufa.
ACF ta bayyana cewa Alhaji Dalhatu ya yi jawabi ne inda ya yi Allah-wadai da ta’addanci, ya kuma yi kira da a kawar da ’yan ta’adda cikin gaggawa.
Kungiyar ta ce bai taba kiran a yi wa ’yan ta’adda afuwa ba, kuma misalin shirin afuwar Yankin Niger Delta da ya ambata shi ne wajen nuna cewa gwamnati na iya amfani da duk wata hanya ta magance matsalar tsaro.
A ƙarshe, ACF ta ce bata taɓa goyon bayan afuwa ga ’yan ta’adda ko ’yan bindiga ba, kuma ta yi watsi da duk wani jita-jita da ke cewa tana marawa irin wannan magana baya.
You must be logged in to post a comment Login