Connect with us

Addini

‘Yan adawa da wasu kamfanonin sadarwa ne ke daukar nauyin farfaganda akan Pantami – Buhari

Published

on

Fadar shugaban kasa ta goyi da bayan ministan sadarwa da bunkasa fasahar tattalin arziki Dr Isa Ali Pantami sakamakon zargin da ake yi masa da furta kalaman goyon bayan kungiyoyin ‘yan ta’adda a shekarun baya.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, ta ce wasu ‘yan siyasa ne da masu kamfanonin sadarwa su ke daukar nauyin farfaganda da ake yadawa kan ministan.

Sanarwar ta ce minista Pantami ya samu abokan hamayya ne sakamakon jajircewa da ya yi wajen nuna kishin kasa da ya ke yi wajen gabatar da tsare-tsare da za su amfanar da al’ummar Najeriya.

Malam Garba Shehu ta cikin sanarwar dai ya kuma ce ko da ya ke kalaman da Pantami ya furta a shekarun baya lokacin yana da karancin shekaru ba su dace ba, amma ai ya nemi afuwa kuma ya canja ra’ayinsa saboda haka fakewa da batagari su ke yi wajen cimma wata boyayyiyar manufarsu ba za ta samu nasara ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!