Labarai
ACReSAL ya fara haƙa Burtsatse a yankunan Bichi da suka jima cikin ƙamfar Ruwa
Gwamnatin jihar Kano ta fara yin aikin gina rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana domin samar da tsaftataccen ruwa tare da magance matsalar rashin ruwan amfanin yau da kullum da al’ummar garuruwan Danya da Ƙyallin Bula ke fuskanta a karamar hukumar Bichi.
Shugaban shirin ACReSAL mai aikin daƙile matsalar kamfar ruwa da matsalolin sauyin yanayi musamman a wuraren tsandauri Dakta Dahir Muhammad Hashim, ne ya jagoranci aikin yayin da ya ke garin tare da tawagar ƙwararru a fannin samar da ruwa, inda kuma bayan gano wurin da ke da ruwa suka fara aikin tona Rijiyoyin a yau Lahadi.
Dakta Dahir Muhammad Hashim, ya bayyana damuwar Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf dangane da matsalolin da al’umma ke fuskanta wajen samun ruwa.
Ya ce, don haka gwamnan ya bayar da umarnin fara gina Rijiyoyin daga yau tare da kammala aikin nan ba da jimawa ba.
Ya ƙara da cewa, gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin lallai mu tabbatar da cewa waɗannan yankuna sun fita daga wannan hali da suke ciki na tsawon shekaru ta hanyar samar musu da ruwa cikin gaggawa.
“Da Asubahin yau Lahadi Mai girma gwamna ya kira ni a waya bayan ya tura mun da wani faifan bidiyo da ya ke yawo a kafafen sada zumunta wanda wata jarida ta wallafa kan irin halin da mazauna wannan yankuna ke shan wahala wajen nemo ruwa” inji Dakta Dahir.
Kuma wannan hali ya na janyo koma baya musamman ga yaran waɗannan garuruwa da ke zuwa ɗiban ruwa waɗanda ya kamata a ce suna makaranta, a cewarsa.
A nasa ɓangaren wakilin mai unguwar Danya Malam Aliyu Ibrahim, ya bayyana cewa sun shafe fiye da shekaru 40 suna fama da wannnan matsala ta rashin ruwa.
Kun ga yanzu na fi shekaru 45 da haihuwa, amma a haka na taso na ganmu cikin wannan matsala kuma haka magabatanmu su ma suka taso cikin halin ƙarancin ruwa, mun sha kai kokenmu ga mahukunta don magance mana wannan hali, sai dai ba mu dace ba, amma yanzu mun gode wa Allah bisa wannan ɗauki da aka kawo mana.
Su ma wasu daga cikin mazauna yankunan sun bayyana cewa mutum kan shafe tsawon wuni guda tun daga Sallar Asubahi har zuwa dare kafin ya samo ruwa a rafin da suke zuwa domin ɗebo ruwan da za su yi amfanin yau da kullum da shi.
Ibrahim Yusuf, matashi ne ɗan asalin garin Danya, ya shaida wa manema labarai cewa a yanzu haka suna sayen ruwan leda watau Pure Water guda ɗaya a kan kuɗi daga Naira 30 zuwa Naira 50.
“Ko a yau da zan yi wanka Naira 150 na sayi ruwa jarka guda mai ɗauke da lita 20 ta ruwa saboda wahalar ruwan da muke ciki” inji Ibrahim Yusuf.
Bayan fara haƙar Rijiyar burtsatsen nan take, tawagar jami’an hukumar ta kuma gano wurin da za a haƙa burtsatsen a garin Ƙyallin Bula wanda ke makwabtaka da garin na Danya inda su ma za a fara haƙa tasu da zarar sun kammala samar da ta garin Danya cikin kwanaki biyu.
You must be logged in to post a comment Login