Connect with us

Coronavirus

Adadin masu Corona ya haura 200 a Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce yanzu haka adadin wadanda suka kamu da cutar Covid-19 ya kai 219 a jihar.

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta wallafa a shafinta na Twitter cewa a ranar Alhamis kadai an samu karin mutane 80 da aka samu na dauke da cutar a jihar.

Har ila yau ma’aikatar lafiyan ta Kano ta nemi al’ummar jihar kan suyi biyayya ga matakan da gwamnati ke dauka domin dakile cutar.

Wannan da na zuwa ne bayan da karin cibiyar gwajin cutar Covid-19 ta biyu a jami’ar Bayero ta fara aiki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!