Kiwon Lafiya
Adadin mutanen da suka rasu a gobarar Masallaci ya ƙaru- hukumar MMSH
Hukumar gudanarwar asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, ta ce, adadin mutanen da suka rasu sakamakon kona wasu masallata a karamar hukumar Gezawa ya karu zuwa goma sha uku.
Shugaban asibitin Dr Hussaini Muhammad, ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin dan takarar shugaban kasa na Jamiyyar LP Peter Obi a farfajiyar Asibitin.
Dr Hussaini ya kuma ce, a yanzu aka akwai mutane Takwas da ke karbar magani sakamakon kunan.
A nasa jawabin, Peter Obi ya ce, ya zo Kano ne domin jajintawa yan uwan wadanda ibtilahin ya shafa tare da adduar ya kiyaye gaba.
Idan za a iya tunawai dai, Shafiu Abubakar mazaunun karamar hukumar Gezawa ne ya kona wasu mutane da ke sallar Asuba a satin da ya gabata.
You must be logged in to post a comment Login