Labarai
Adadin wadanda suka kamu da cutar lassa a Najeriya ya kai 846- NCDC
Hukumar dakile yaduwar cututtuka masu yaduwa ta Nijeriya NCDC, ta ce, zuwa yanzu adadin wadanda suka kamu da zazzabin Lassa a kananan hukumomi 99 na jihohi 25 na sun kai dari 846.
Hakan na cikin rahoton da NCDC ke fitarwa a kowanne mako, wanda aka fitar a yau Alhamis.
A cewar NCDC, wadanda ake zargin sun kamu da cutar Lassa, adadin ya kai dubu 4,338, sai kuma mutane 148 da suka rasu sanadiyyar cutar a fadin kasar nan.
Cikin rahoton ya nuna cewa, rukunin wadanda suka fi kamuwa da cutar Lassa shekarunsu ya fara daga 21 zuwa 30, kuma cutar na ci gaba da yaduwa sakamakon cin wasu kwayoyin cuta a cikin abinci, ko kuma muhallin da bashi da tsafta.
Haka kuma tsakanin 27 ga watan Maris zuwa biyu ga watan Afrilun da muke ciki, mutane 23 ne suka kamu da cutar a jihohin Bauchi da Ondo da Edo da Taraba sai Ebonyi da Oyo sai kuma jihar Kebbi.
You must be logged in to post a comment Login