Labaran Wasanni
AFCON 2021: Ƙasar Senegal ta lashe gasar a karo na farko
Kungiyar kwallon kafa ta kasar Senegal ta lashe gasar cin kofin kasashen afrika ta AFCON ta shekarar 2021.
Wasan dai ya gudana a ranar Lahadi 06 ga Fabrairun 2022 a filin wasa na Olambe da ke kasar Kamaru, inda Senegal tayi nasara a bugun daga kai sai mai tsaran gida.
Dan wasa Sadio Mane ne dai ya tabbatar da nasarar kasar ta Senegal bayan da ya zura kwallo a bugun na daga kai sai mai tsaran gida.
Tinda fari dai wasan an shafe minti 90 ba ta reda ko wacce kungiya ta samu nasarar zura kwallo a ragaba.
Sai dai a minti na 7 dan wasan Sadio Mane ya gaza zura kwallon da kungiyarsa ta samu a bugun daga kai sai mai tsaran gida, bayan da mai tsaran gida Gabaski ya hana kwallon shiga raga.
Nasarar lashe gasar da kasar Senegal tayi ya sa jumulla ta lashe a karo na farko a tarihi, bayan da a shekarun 2002 da kuma 2019 ta gaza lashe gasar.
Gasar AFCON dai ta shekarar 2021 wadda ake gudanarwa a shekarar 2022 itace karo na 33 jumulla.
You must be logged in to post a comment Login