Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

AFCON 2022: A shirye Najeriya take ta fuskanci ko wacce kasa – Ahmed Musa

Published

on

Kyaftindin  kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles Ahmed Musa ya ce tawagar a shirye ta ke data fuskantar ko wacce kasa a gasar cin kofin Afrika da ake gudanarwa halin yanzu a kasar Kamaru ta shekarar 2021.

Zakarun gasar har sau uku tuni suka tsallaka zuwa zagaye na 16 bayan nasara akan Sudan da ci 3-1 a ranar Asabar.

Tin da fari dai kasar Kamaru ce ta fara kaiwa zagaye na 16, kana itama kasar Morocco ta samu damar kaiwa bayan nasara a kan Comoros.

“Matuka nayi farinciki da murna sakamakon nasarar da muka samu na wasanni biyu, wanda haka ne ya sa tawagarmu ta zama ta musamman a gasar,” a cewar Musa.

“Wannnan dalilin ya sa yanzu zamu dage kuma babu wata kasa da zamuyi shakkar haduwa da ita gasar da ake gudanarwa”

“Abin da ya rage mana shi ne yadda zamuyi shiri da kuma kalubalen da zamu fuskanta a wasannin zagaye na 16 da zamu fafata,” a cewar Ahmad Musa.

Zuwa yanzu dai Super Eagles na mataki na farko a rukunin D da maki 6 a wasanni 2, inda zata kara da Guinea-Bissau a wasan karshe na rukunin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!