Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

AFCON 2023: Najeriya ta lallasa Sao Tome and Principe da ci 10-0

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles ta lallasa kasar Sao Tome and Principe da ci 10-0 a wasan neman cancantar zuwa gasar cin kofin kasashen Nahiyar Afrika ta shekarar 2023.

Andai fafata wasan ne tsakanin tawagar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles da kasar Sao Tome and Principe a filin wasa na Stade Agadir dake kasar Morocco.

Kuma shine karon farko da Najeriya ta sami irin wanan gagarumar nasarar tun bayan data lallasa kasar Benin da ci 10 da 1 a shekarar 1959.

Dan wasa Victor Osimhen ne ya jefa kwallo hudu a mintuna 9 da 48 da 65 da kuma 84 sai dan wasa Moses Simon da ya ci a mintuna na 28th inda shima dan wasa Tareem Moffi ya ci a minti 43 da 60, shi kuwa Oghenekaro Etebo ya zura kwallo a mintuna na 55.

Yayin da dan wasa Ademola Lookman ya ci a mintuna na 63 sai kuma Emmanuel Dennis da ya ci shima a mintuna na 90.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!