Labarai
AFDB : An wanke shugaban bankin raya kasashen Afrika daga zargi
Kwamitin kwararru wanda tsohuwar firaministan kasar Ireland Mary Robinson ta ke jagoranta ya wanke shugaban bankin raya kasashen Afirka AfDB Akinwumi Adesina.
A cewar kwamitin Mista Akinwumi Adesina ba shi da laifi a zargin cin hanci da ake yi masa.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa, a farkon wannan shekarar da muke ciki ne wani rahoto mai shafi goma sha biyar ya zargi Mista Adesina mai shekaru sittin da laifin nuna fifiko gda rashin iya shugabanci da kuma arzuta kansa.
Sai dai kwamitin kwararrun da Robinson ta jagoranta tare da babban mai shari’a na kasar Gambia Hassan Jallow da kuma mataimakin shugaban gwamnan bankin duniya mai kula da bangaren nagartar aiki Leonard McCarthy, sun wanke tsohon ministan noman na Najeriya daga dukkannin zarge-zarge da ke kansa.
A baya dai kasar Amurka ce ta dage kan dole sai an binciki mista Adesina kan zargin, biyo bayan wankeshi da hukumar gudanarwar bankin na AfDB ta yi, lamarin da ya sa a kafa kwamitin kwararru don gudanar da binciken kan badakalar.
You must be logged in to post a comment Login