Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ahmed Musa zai taimaka wa Pillars lashe kofin bana – Ganduje

Published

on

Gwamnan Kano Dakta Anbdullahi Umar Ganduje, ya ƙaddamar da kyaftin ɗin tawagar Super Eagles ta Najeriya, Ahmad Musa a matsayin sabon ɗan wasan tawagar Kano Pillars.

A wani ƙwarya-ƙwaryar taro na masu ruwa da tsaki a harkar ƙwallon ƙafa da wasanni, da ya gudana ranar Jumu’a a fadar Gwamnatin jihar, gwamna Ganduje ya gabatar da ɗan wasan biyo bayan amincewa da ɗan wasan ya yi tare da saka hannu kan kwantiragin wakiltar tawagar zuwa ƙarshen gasar kakar Firimiya ta Najeriya NPFL 2021.

“Babu shakka dawowar ka zuwa Kano Pillars ya nuna ƙaunar ka da kishin ka a kan ƙungiyar da kuma tuna baya da ka yi”.

“Kai sananne a duniya gaba ɗaya, tabbas mun yi babban kamu, zamu ci gaba da taimakawa tawagar, kai ma muna fatan zaka taimaka wajen ganin ƙungiyar ta lashe kofi na Najeriya nan gida Kano “ inji gwamna Ganduje.

Daga cikin waɗanda suka karɓi dan wasan tare da taimakawa gwamnan wajen ƙaddamar da ɗan wasan, akwai shugaban hukumar wasanni ta jihar Kano Alhaji Ibrahim Galadima.

Sai Kwamishinan Wasanni Kabiru Ado Lakwaya da Mataimakin Gwamna Nasiru Yusuf Gawuna da shugaban ƙungiyar Kano Pillars, Alhaji Shu’aibu Surajo Yahaya Jambul.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!