Labarai
Aikin Allah: Ganduje zai yiwa ƴan Hisbah ƙarin albashi

Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin yin ƙarin albashi ga jami’an hukumar Hisbah.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi, yayin fasa kwalaben giya da Hisbar ta kama.
Gwamnan ya samu wakilcin mataimakinsa Nasir Yusuf Gawuna.
Hoto yayin fasa kwalaben giyar
Gawuna ya nemi ƴan Hisbah da su ci gaba da dagewa a kan aikinsu.
“Gwamnati zata canja wa ƴan Hisbah kayan sarki, (kaki) sannan gwamnati zata ci gaba da basu goyon bayan wajen gudanar da aikinsu na hidimtawa addini” a cewarsa.
Babban Kwamandan Hisbah Malam Haruna Ibn Sina ya ce, gabanin fasa giyar sai da suka samu amincewar kotu.
Hoto yayin fasa kwalaben giyar
You must be logged in to post a comment Login