Labaran Kano
AKTH ya gudanar da aikin yanar ido ga mutum 250
Asibitin koyarwa na malam Aminu Kano ya gudanar da aikin yanar ido ga marasa karfi 250 a karamar hukumar Dawakin Kudu dake nan jihar Kano.
Da yake zantawa da manema labarai shugaba da ke lura da shirin na taimakawa marasa karfi Dr Sadiq Hassan wanda shi ne shugaban sashen kula da idanu ya ce, burinsu shi ne gudanar da aikin yana ga kimanin mutane da ke faaa da lalurar su 500.
Dr Hassan ya kara da cewa asibitin zai bada gilashin idanu ga kimanin masu lalurar gani fiye da 3000 baya ga wadanda za’a baiwa magani su 3000.
Haka kuma ya kara da cewa an turo musu masu fama da matsalar yanar ido domin basu kula ta mussamam bayan da aka kasa basu kulawar da ta dace daga karamar hukumar Dawakin Kudu.