Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

WorldSightDay: An yiwa masu larurar ido aiki kyauta a Kano

Published

on

Asibitin idanu na Makka da ke nan Kano, ya gudanar da aikin idanu kyauta tare da yin gwaje-gwaje ga masu fama da lalurar idanu a wani mataki na saukakawa al’umma halin matsin rayuwa da suke ciki.
Shugaban asibitin Alhaji Yusuf Ahmad ne bayyana hakan a yau lokacin da ya ke kaddamar da yiwa masu fama da lalurar idanu kyauta a wani bangare na bikin ranar idanu ta duniya da a ke gudanarwa a yau.
Wasu da suka ci gajiyar aiki tare da magani kyauta sun bayyana farin cikin su bisa taimakon da aka yi muus.
Wakilinmu Yusuf Ali Abdallah ya rawaito cewa asibitin ya karbi marasa lafiyar idanu daga kananan hukumomi arba’in da hudu na jihar Kano, inda kuma aka yi musu gwaji da basu magani kyauta yayin da wasu kuma za a yi musu aiki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!