Labarai
Akwai ‘yan bindiga sama da dubu talatin a jihar Zamfara – Majalisar Sarakuna

Majalisar sarakunan gargajiya ta jihar Zamfara ta ce akwai ‘yan bindiga a dazukan jihar sama da dubu talatin.
Sarakunan sun bayyana hakan ne lokacin da suke ganawa da manyan hafsoshin tsaron kasar nan wadanda suka kai ziyara a jihar ta Zamfara a jiya Talata.
Rahotanni sun ce ya zuwa yanzu sojoji dubu goma ne kacal ke aikin samar da tsaro a jihar.
You must be logged in to post a comment Login