Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Akalla akwai ‘yan bindiga dubu 30 a jihohin arewa maso yamma – Matawalle

Published

on

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya ce akwai ‘yan bindiga akalla guda dubu talatin a jihohin arewa maso yamma.

A cewar gwamnan na Zamfara akwai kuma sansanonin ‘yan bindiga akalla guda dari a dazuka dake jihohin.

Wanda a cewar sa kowane daya daga cikin sansanonin yana kunshe da ‘yan bindiga akalla guda dari uku.

Gwamnan na Zamfara wanda kwamishinan kananan hukumomin jihar Alhaji Ibrahim Magaji Dosara ya yi magana a madadinsa, ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai ranar juma’a a garin Kaduna.

Ya kuma bayyana jihohin da ‘yan bindigar suke da sansanoni da cewa sun hada da: Zamfara, Sokoto, Kebbi, Katsina, Kaduna da kuma Niger.

Gwamnan na Zamfara ya kuma ce gwamnatin tarayya ba ta da isassun sojoji da za ta iya samun galaba akan ‘yan bindigar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!