Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Akwai yiwuwar bude makarantun boko

Published

on

A yau ne ake saran cewa gwamnatin tarayya da na jihohi za su gana wajen sake yin nazari kan  bin dokokin da aka sanya musu, domin yanke shawarar ranar da za’a bude makarantu a kasar nan.

A dai kwanakin baya ne ma’aikatar ilimi ta kasa ta aikewa shugabanin makarantu kundin bayanai mai dauke da shafuka 52 na bin dokokin da aka shifida musu da zai baiwa dalibai na karshe rubuta jarrabawar a makaratu duk da annobar Corona da ake fama da shi a kasar nan.

Babban sakatare a ma’aikatar ilimi  Mr. Sonny Echono ya sanar da hakan cewa, da zarar an kammala ganawar ne ake saran cewar za’a sanar da ranar da za’a bude makarantu a Najeriya.

Ganawar wacce za’a yi ta kafar Internet tare da hukumomin ma’aikatar ilimi da kwamishinonin ilimi na jihohin kasar nan 36  har da na babban birnin tarayya Abuja.

Mr Sonny Echono ya kara da cewar daga cikin wadanda ake sa ran za su shiga ganawar akwai, hukumomin masu shirya jarrabawa ta kasa NECO da WAECO da kuma NABTEB.

Sauran su ne kungiyar Shugabanni makarantu masu zaman kan su ta kasa NAPPS da kuma ANCOPSS da dai sauran su.

A dai makwan da ya gabata ne karamin ministan ilimi Emeka Nwajiuba ya sanar da cewar, an baiwa Najeriya zabin rubuta jarrabawar karshe ta kammala sakandire ta kasa daga watan Nuwanba zuwa Disamba.

.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!