Labarai
Akwai yiwuwar Muhuyi Magaji zai yi Idi a gidan gyaran hali
Hukumar lura da manyan Kotunan Kano ta musanta rahoton cewa ta yi jan ƙafa wajen aiwatar da belin Muhyi Magaji da Kotu ta bayar.
Kakakin Kotunan Kano Baba Jibo Ibrahim be ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio.
Baba Jibo wanda ke martani kan wasu rahotonni da aka yaɗa da suka ce, Muhuyin ya cika sharuɗan da Kotu ta sanya masa amma jami’an kotu suka hana belinsa.
“Babu wani haɗin baki tsakanin Kotu da wasu shugabannin, Kotu ta tsaya ta yi aikinta kamar yadda doka ta tsara mata”. A cewarsa.
Ya ƙara da cewa, Muhuyi Magaji bai samu cika sharuɗan belin a kan lokaci ba, har sai bayan kotu ta tashi, shi ne abin da ya kawo tsaiko.
A yau ne ƴan sanda suka gurfanar da Muhyi Magajin a gaban Kotun Majistiri mai lamba 58 bisa zarginsa da bayar da takardun lafiya na bogi.
Sai dai Kotu ta bada belinsa bisa sharuɗan zai ajiye kuɗi har Naira Dubu Ɗari Biyar, da shaidar biyan haraji na shekaru uku da kuma Fasfo ɗinsa na banki.
Da kuma mutane biyu, ciki ɗaya ya zama mahaifinsa ko limamin masallacin Juma’a na Sharaɗa ko Ja’en, ko Dagacin Sharaɗa.
To sai dai da alamu Muhuyin zai yi idi a gidan gyaran hali, saboda gaza cika sharuɗan a yau Jumu’a, kasancewar gobe za a shiga hutun ƙarshen mako da hutun sallah.
You must be logged in to post a comment Login