Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Akwai yiwuwar rushe gadar Ƙofar Nassarawa – Ganduje

Published

on

Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce, akwai yiwuwar ya rushe gadar sama ta Ƙofar Nassarawa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin Kwamishinan yaɗa labarai na jiha Malam Muhammad Garba yayin ziyarar da ƙungiyar Ganduje Raya Kano Yake ta kai masa.

Muhammad Garba ya ce, tuni suka shiga nazari tare da ƙwararru kan irin matsalolin da gadar ke haifar wa ga al’ummar Kano.

Sannan gadar ta fara zaizayewa saboda rashin kyawun aikin da aka yi.

Kwamishinan ya ce, da zarar ƙwararru sun gama nazari a kai Gwamnati za ta duba yiwuwar rushe gadar tare da sake ta.

Muhammad Garba ya ce, ayyukan Gwamnatin baya ayyuka ne marasa kan gado waɗanda ba a yi amfani da ilimi ba wajen aiwatar da su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!