Labarai
Akwai yiwuwar samun daidaito tsakanin KAROTA da Ƴan Adaidaita
Rahotonni daga hukumar KAROTA na cewa ana gab da samun daidaito tsakanin hukumar da masu baburan adaidaita sahu.
Hakan dai ya biyo bayan shiga tsakani da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa NLC ta yi.
Wata majiya ta shaida wa Freedom Radio cewa, yayin zaman da a kayi da masu ruwa da tsaki a hukumar a ranar Talata an tattauna muhimman abubuwa kan yadda za a samu daidaito a tsakanin ɓangarorin biyu.
Labarai masu alaka:
Haƙiƙanin abin da ke faruwa tsakanin KAROTA da Ƴan Adaidaita
Zamu sasanta rikicin KAROTA da ‘Yan adaidata sahu – NLC
Mai taimaka wa Gwamnan Kano kan KAROTA Nasiru Usman Na’ibawa ya ce, tuni tattaunawar ta yi nisa.
A cewar sa, nan ba da jimawa ba ƙungiyar ƙwadago za ta fitar da sanarwa kan matsayar da aka cimma.
A ranar Litinin ne masu baburan adaidaita sahu suka tsunduma yajin aiki a Kano kan batun tsarin biyan kuɗin haraji.
Yanzu dai abin jira a gani shi ne, ko matsayar da za a cimma za ta yi tasiri a tsakani.
You must be logged in to post a comment Login