Labarai
Akwai yuwar samun ambaliyar ruwa a Kano – Masani
Daga Mu’azu Tasi’u Abdurrahman
Wani masani kan al’amuran da suka shafi labaran kasa na jami’ar Yusif Maitama Sule dake nan Kano ya bayyana cewa akwai yuwar samun ambaliyar a wasu kananan hukumomin jihar Kano, sakamakon sauyin da aka samu wajen amfani da Koguna mussaman ma a damunar bana.
Malam Nazifi Umar Alaramma ne ya bayyana haka ta cikin shirin Duniyar mu a yau na nan Freedom radio da ya mayar da hankali kan rahoton da hukumar kula da hasashen masana yanayi ta kasa ta fitar a kwanakin baya cewa, akwai yuwar samun ambaliyar ruwa a wasu kananan hukumomin jihar kano guda ashirin 20.
Malam Nazifi Umar Alarmma ya ce akwai kanshin gaskiya a cikin wannan hasashen da ake yi na yiyuwar samun ambaliyar ruwa musamman a kananan hukumomin dake cikin kwaryar birnin Kano, sakamakon datse magudanar ruwan da ake yi a mafi yawan lunguna da sako na cikin birnin.
Ya ce matukar mutane ba za su yi hattara wajen daina gine-gine akan magudanan ruwa tare da gyara su ba, to shakka babu ruwan zai samarwa kansa hanya ta hanyar afkawa cikin gidajen mutane.
A nasa bangaren babban darakta na hukumar raya Kogin-Hadejia Jam’are Dr, Ado Khalid Abdullahi da ya kasance a cikin shirin ya bayyana cewa, a halin da ake ciki hukumarsu tana gudanar da gyare-gyare a cikin kogin Hadejia Jam’are wanda hakan ne yasa tilasta suka datse ruwan da hukumar ke sakowa a kewayen jihohin Jigawa da Kano domin amfanin manoma, wanda hakan zai taimaka wajen takaita iftila’in ambaliyar ruwan da ake hasashen samu a bana.
Dr Ado khalid Abdullahi ya kara da cewa rashin yashe Dama-daman da ake da su a yawancin kananan hukumomin dake wajen gari na taimakawa wajen samun ambaliyar ruwa a wadannan kananan hukumomi dake yankunan, inda ya ta’allaka al’amarin da sakacin gwamnatocin da suka gabata.
Bakin dai sun ja hankalin al’umma da su kaucewa yin gine-gine a kan magudanar ruwa don gudun fadawa mawuyacin hali a nan gaba dama damunar ta Bana.
You must be logged in to post a comment Login