Labarai
Al-mundahana: An yankewa ‘yan kasuwa 5 hukuncin zaman gidan kaso
Daya daga cikin kotunan tafi da gidanka karkashin kwamitin tsaftar muhalli na jihar Kano ta yankewa wasu ‘yan kasuwa 5 hukuncin zaman gida kaso na tsawon wata guda tare da biyan tarar Naira dubu goma.
Mai shari’a Auwal Muhammad ne ya yanke sakamakon kamasu da laifin sayar da garin rogo mara kyau ga al’umma a kasuwar ‘yan kura da ke sabon gari.
Tun da fari dai dakarun tsaftar muhalli ne suka kama buhunhunan garin rogo guda 30 a shagunan ‘yan kasuwar.
Hakan na cikin wata sanarwar da mai magana da yawun ma’aikatar muhalli ta jihar Kano Abbas Habeeb Abbas ya raba ga manema labarai.
Alhaji Ahmad Ja’afaru Gwarzo shi ne sarkin tsaftar jihar Kano ya ce dakarun tsaftar muhalli sun bankado mutanen ne lokacinda suke ran-gadin kasuwanni don tabbatar da ingancin kayan da ake sayarwa.
Yace daya daga cikin wadanda ake zargi ya tsere, sai dai tuni ma’aikatar muhalli ta jihar Kano ta bada umarnin lalata kayan don kare al’umma daga cin abinda zai haifar musu da illa.
You must be logged in to post a comment Login