Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An samu tashin gobara a ma’aikatun gwamnati 20 a shekarar nan – Minista

Published

on

Gwamnatin tarraya ta ce, an samu gobara a ma’aikatun gwamnati da ma masu zaman kansu har sau 20 daga farkon shekaran nan zuwan watan Octoban da muke ciki.

Ministar jin kai da kare aukuwar ibtila’i da ci gaban al’umma Hajiya Sadiya Umar Faruk ce ta bayyana hakan, yayin zantawa da manema labarai a birnin tarraya Abuja.

A cewar ta, an samu dimbin asarar dukiya a sakamakon gobarar sakamakon sakaci da rashin kula da kayan lantarki a ma’aikatun.

Hajiya Sadiya Umar Faruk ta ce, a yanzu haka gwamnatin taryya ta shirya tsare-tsare wayar da kan ‘yan kasa hanyoyin kare aukuwar gobara a gidaje da masa’antu har ma da ma’aikatu la’akari da yanayin sanyi da ke karatowa.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!