Labarai
Algus din takin zamani na barazana ga amfanin gona – Masani
Wani mai masana’antar takin zamani a nan Kano Alhaji Ibrahim Hussain Abdullahi, yayi Alla-wadai da yadda wasu ke canjawa buhunhunan takin zamani suna da bayanan hakkin mallaka, sannan su sanya taki marasa inganci a ciki su sayarwa da manoma.
Alhaji Ibrahim Hussain Abdullahi ya bayyana hakan ne, yayin da yake zantawa da manema labarai, inda ya ce abin takaici ne matuka yadda wasu bata-gari ke cutar da manoma ta hanyar sayar mu da taki mara kyau da aka canza masa buhu.
Wannan na zuwa ne dai-dai lokacin da damuna ke kara kankama, inda manoma kan bazama neman taki domin inganta amfanin gonar su.
You must be logged in to post a comment Login