Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za a rage farashin takin zamani

Published

on

Gwamnatin tarayya tace sakamakon karyewar tattalin arziki saboda annobar corona musamman ma a tsakanin manoma ne yasa ta rage farashin takin da take samarwa daga naira dubu biyar da dari biyar zuwa dubu biyar.

Shugaban kwamitin samar da takin gwamnatin tarayya kuma gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ne ya bayyana hakan a yau Litinin yayin da ya kawo ziyarar duba kamafani samar da takin zamani na jihar Kano.

Ya kuma ce duk takin da manoma suka saya da gwamnatin ke samarwa a farashi sama da dubu biyar to su sanarwa da jamian tsaro.

Da yake jawabi Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya godewa gwamnan na Jigawa bisa ga ziyartar kamfanin da yayi na duba kamfanin tare da kuma duba ingancin takin da ake samarwa.

Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kuma kara da godewa gwamnan Jigawa bisa ga kokarin da yakeyi na ganin taki ya wadata a kasar nan.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!