Labarai
Alkhairi Orphanage ta ƙaddamar da rabon kayan abinci da na Sallah ga ma buƙata 500
Ƙungiyar tallafa wa mata da marayu ta Alkhairi Orphanage and Women Development, ta ƙaddamar da rabon kayan abincin Azumi da kuma kayan Sallah ga mutane 500 da suka haɗa da mutane marasa ƙarfi da masu buƙata ta musamman su 350,da kuma yayata marayu su 150 da ta fara basu kayan Sallah.
Yayin ƙaddamar da rabon a Asabar ɗin nan, shugabar ƙungiyar Kwamared Ruƙayya Abdurrahman, ta bayyana cewa, irin wannan tallafi na daga cikin ayyukan da ƙungiyar ta shafe shekaru da dama ta na gudanarwa.
Haka kuma ta ƙara da cewa, “Daga cikin ayyukan wannan ƙungiya bayan kula da karatu da kuma lafiyar yara marayu, akwai yaƙi da cin zarafin ƴaƴa mata da koyar da sana’o’in dogaro da kai da kuma wayar da kan mata masu ɗauke da juna biyu da sauransu.”
“Mun kashe fiye da Naira dubu 500 wajen sayan kayan Sallah ga marayu a bana, sannan mun samu tallafin kayan abinci daga kamfanin Fulawa mai Kwabo, sannan mun samu tallafi daga Makaman Bichi Alhaji Isiyaku Umar Tofa sai kuma shugaban asibitin koyarwa na Aminu Kano Dakta Abdurrahman Abba Sheshe da kima kamfanin MC Plastic, dukkan su muna godiya da fatan Allah ya saka musu da alkhairi” inji Kwamared Ruƙayya Abdurrahman.
A nasa ɓangaren, Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Kano Alhaji Lawan Hussaini Chediyar ƴan Gurasa, da ya halarci taron, kira ya yi ga al’umma musamman mawadata, da su riƙa tallafa wa marayu da masu ƙaramin ƙarfi har ma da mutane masu buƙata ta domin sauƙaƙa musu halin matsin rayuwa da ake fuskanta.
Ɗan majalisar ya ce, “Na yi matukar farin ciki da na ga yadda mutane suka taro domin karɓar wannan tallafi, wannan ya ja hankalina in yi kira ga al’umma da a rika tallafa wa da duk abinda ya samu komun ƙanƙantarsa”.
Shi ma mataimakin babban kwamandan Hisbah na Kano Dakta Mujahiddin Aminuddin, a nasa jawabin, ya yaba wa ƙungiyar tare da yin kira ga mutane da su riƙa yin koyi da ita wajen tallafa mutane musamman ma marayu domin tallafar rayuwarsu.
Malam, Sulaiman Zubairu, shi ne Sakataren gamayyar ƙungiyar mutane masu buƙata ta musamman, ta jihar Kano, ya bayyana godiya bisa tallafin ya na mai cewa, “Babu abinda za mu ce da Kwamared Ruƙayya sai godiya, ta kira ni ta ce na kawo mutanena su karɓi tallafi, kuma ga shi ana bayarwa, Allah ya saka mata da alkhairi.
You must be logged in to post a comment Login