Labarai
Almajirai 4 sun rasu sakamakon cin gurbataccen abinci a Kano

Almajirai huɗu na Tsangayar Malam Iliyasu Mai Tsangaya da ke Kadage Sharifai a Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano sun rasu bayan cin abincin da ake zargin gurɓatacce ne.
Shugaban ƙungiyar Tsangaya Media Network ta ƙasa Alaramma Sani Musa Nuhu, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwar ta ce, almajiran sun rasu ne a Asibitin Malam Aminu Kano a daren Lahadi, 16 ga Agusta, 2026, bayan sun ci abincin da ake zargin ya gurɓata.
Sanarwar ta ƙara da cewa, an gudanar da jana’izar almajiran bayan samun umarni daga Dagaci da baturen ƴan snadan yankin.
You must be logged in to post a comment Login