Connect with us

Labarai

Majalisar dokokin Kano ta buƙaci a gyara babban ɗakin karatu

Published

on

Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta karɓi ƙudirin neman a gyara tare da zamanantar da ɗakin karatu na Murtala Muhammad Library da ke nan jihar Kano.

Nabil Aliyu Daneji, Ɗan Majalisa mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Birni ne ya gabatar da ƙudirin, inda ya ce ɗakin karatun na buƙatar gyara duba da yadda kayayyakin da ke cikinsa da kuma ginin wurin suka lalace.

Ɗan majalisar ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta ɗauki matakin gyara tare da zamanantar da ɗakin karatun, musamman ta hanyar samar da na’urorin kwamfuta da sauran kayan zamani da za su inganta ayyukansa.

Ƙudurin dai, ya samu goyon bayan ɗan majalisa mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Ungogo, Sa’ad Aminu Sa’ad tare da bawa kwamitin ilimi zurfi da ya je don duba halin da ɗakin karatun ke ciki tare da gabatar da rahoto a gaban majalisar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!