Labarai
Neja: Manoma biyar sun Rasu sakamakon kifewar Kwale-kwale

Manoma biyar, maza huɗu da mace ɗaya, sun mutu bayan wani kwale-kwale ya kife a Kogin Kudi, a Ƙaramar Hukumar Katcha ta Jihar Neja da ke arewacin Nijeriya.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar a ƙauyen Shaba-Woshi-Kpaya, da ke gundumar Edotsu, a cewar ganau.
Wani mazaunin yankin, Muhammadu Dan-Asabe, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa mutanen suna kan hanyarsu ta zuwa gonakinsu ne lokacin da kwale-kwalen ya kife.
Daraktan Yaɗa Labarai da Ayyuka na Musamman na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Dr
Ibrahim Audu Hussaini, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce waɗanda abin ya rutsa da su suna tafiya ne daga ƙauyensu zuwa gonakinsu lokacin da kwale-kwalen ya kife.
You must be logged in to post a comment Login