Labarai
Almundahana: Kotu ta yankewa Abdurrashid Maina hukuncin shekara 61 a gidan gyaran hali
Babbar Kotun tarayya mai zamanta a Abuja ƙarkashin jagorancin mai shari’a Okon Abang, ta zartar da hukuncin ɗaurin shekaru 61 ga tsohon shugaban kwamitin gyaran fansho na tarayya Abdulrashid Maina.
Kotun ta yanke hukuncin ne sakamakon samun Abdulrashid Maina da laifin halasta kuɗaɗen haram, ta hanyar hada baki da wani ma’aikacin banki na Fidelity wajen buɗe asusun bogi.
Sannan Kotun ta same shi da laifin ɓoye sunansa wajen buɗe asusu a bankin UBA da kuma Fidelity, inda ya ƙoye naira miliyan 300 sannan ya sake sanya naira miliyan 500, ya kuma ƙara sanya naira biliyan ɗaya da rabi.
Kotun ta ce waɗannan kuɗaɗe da ya ɓoye a bakunan ya kwashe su ne daga asusun kwamitin gyaran fansho da shugaban ƙasa ya kafa.
Haka zalika Kotun ta ce hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa EFCC ta gabatar da gamsassun shaidun da suka tabbatar da cewa Abdulrashid Maina ya aikata laifin halasta kuɗaɗen haram da suka haura naira miliyan 171.
You must be logged in to post a comment Login